Barka da zuwa shafin AREWA TALENT, A wannan lokaci Insha Allahu zamu nuna maka yanda zaka kirkiri blog website cikin sauki, Amma kafin nan a baya munyi bayani akan wana abubuwa yakamata kasani kafin kafara sana’ar blogging, Domin sanin wana abubuwa danna link dake kasa.
Read More: [Blogging] Wana Abubuwa Yakamata Kasani Yayin da Zaka Fara Sana'ar Blogging 2020.
How to create a blog.
Step 1: Abu na farko da zaka farayi shine zaka shiga
cikin browser dinka, Saika saka wannan address din dazan baka www.blogger.com
saika danna search bayanka danna search daga baya kuma zai bude maka wani shafi
kamar haka.
Step 2: Abu na Biyu da zaka karayi shine bayan ya
bude maka shafin a shafin zakaga wani rubutu daga tsakiya ansa | Create Your Blog |
daga sama kuma a gefe zakaga ansa | Sign In | saika shiga daya daga cikin
wadannan rubutun. Bayanka shiga zai bude maka wani shafin kamar haka.
Step 3: Abu na Uku da zaka karayi shine, Bayanka
shiga zai baka damar kasaka Gmail Account dinka idan kana dashi idan kuma baka
dashi zakaga wani rubutu an saka | Create Account | saika shiga kabude, Idan
kuma kana dashi saikayi Login dashi, kana shiga zai bude maka wani shafin kamar
haka.
Step 4: Abu na Hudu da zaka karayi shine, Bayan ya
bude maka wannan shafin a shafin daga kasa zakaga ansa | Create New Blog |
saika danna shi bayanka danna zai nuna maka wani shafi kamar haka.
Step 5: Abu na Biyar da zaka karayi shine, Bayanka
danna zai baka damar kasaka Title din sunan da kakeso ya dinga fitowa a saman
blog dinka, Bayanka gama saka Title din, a kasa kuma zakaga ansa Address shi
kuma wannan shine sunan da zaka saka idan anyi searching din website dinka za’a
dinga ganinka.
Bayanka gama saka duk wadannan abubuwa daga kasa zakaga
ansa Create Blog saika danna shi kana dannawa shikenan ka kirkiri website, Anan
zamu tsaya nan gaba kuma zamu kawo muku darasin koyon blogging kashi na biyu.
Read More: [MTN] Yadda Zaka Siyi Datar MTN 1GB N200 da Kuma 2GB N500 2020
Ku Kasance Da Arewa Talent A Kowane Irin Lokaci Muma Zamu Cigaba Da Kawo Muku Abubuwa Wanda Zaku Dinga Karuwa Dasu Kuma Kuna Jin Dadinsu, Nine Naku Aminu B Yusuf CEO Founder Na Arewa Talent.
Domin Neman Karin Bayani Ko Kuma Bamu Wata Shawara Akan Wani Abu Zaku Iya Tuntubarmu Ta Wadannan Hanyoyi Kamar Haka.
Email: aminubyusuf20@gmail.com
WhatsApp: +2347010942309
Facebook: Arewa Talent
Instagram: ArewaTalent.Com.Ng
YouTube Channel: Arewa Talent Tv
Comments
Post a Comment