[Blogging]: Darasin Koyon Blogging Kashi Na Biyu 2020

How to create pages on blogger

Barka da zuwa shafin Arewa Talent, A wannan lokaci Insha Allahu zamu cigaba da darasin mu na koyon blogging, a baya munyi Magana akan yadda ake bude blog yanxu kuma zamu shiga darasin mu nagaba.

Read more: [Blogging]: Wana Abubuwa Yakamata Kasani Yayin da Zaka Fara Sana'ar Blogging 2020.

Read more: [Blogging]: Darasin Koyon Blogging Kashi Na Farko 2020

Wannan darasin da zamu shiga zamuyi Magana ne akan wasu abubuwa guda hudu wanda idan harka bude blog yakamata kasaka su, Saboda suna da mutukar mahimmanci a blog sosai.

Abinda muke nufi shine zamu nuna maka yadda ake saka wadannan abubuwa a saman header na blog dinka About Us, Contact Us, Privacy Policy da kuma Sitemap.

How to create pages on blogger?

Step 1: Abinda zaka farayi shine idan kashiga cikin dashboard dinka na blog daga gefan hannunka na hagu zakaga wasu rubutu, Acikin wadannan rubutu zakaga ansa Pages saika danna shi kana dannawa zai bude maka wani shafin.

Step 2: Abu na biyu da zaka karayi shine bayanka danna ya bude maka wani shafin a shafin daya bude maka zaka wani wuri ansa Create New Page ko kuma New Page, saika danna daya dagacin wadannan abubuwa, kana dannawa zai bude maka wani shafin.

Step 3: Abu na uku da zaka karayi shine bayan kadanna ya bude maka wani shafin, Acikin wannan shafin daga sama zakaga ansa Page Title saika danna wurin kana dannawa zai baka damar kasaka sunan Page din da kakeso,

Step 4: Abu na hudu da zaka karayi shine bayan kasaka sunan da kakeso a sama daga gefan hannunka na dama zakaga ansa Publish saika danna shi kana dannawa shikenan ya zauna.

Step 5: Abu na biyar da zaka kara shine bayanka bude duk wadannan abubuwa, daga gefan hannunka na hagu zakaga ansa Layout saika danna shi kana dannawa zai bude maka wani shafin, acikin shafin zakaga ansa Page List Top saika danna shi kana dannawa zai bude maka wani shafi acikin shafin zakaga duk shafin daka kirkira.

Step 6: Abu na shida da zaka karayi shine bayanka ga duk Pages daka kirkira daga sama zakaga ansa Select All saika danna shi kana dannawa shikenan sai kuma daga kasa zakaga ansa Save saika danna kana dannawa shikenan kagama.

Idan baka gane ba zaka iya kallon wannan video

Ku Kasance Da Arewa Talent A Kowane Irin Lokaci Muma Zamu Cigaba Da Kawo Muku Abubuwa Wanda Zaku Dinga Karuwa Dasu Kuma Kuna Jin Dadinsu, Nine Naku Aminu B Yusuf CEO Founder Na Arewa Talent.

Domin Neman Karin Bayani Ko Kuma Bamu Wata Shawara Akan Wani Abu Zaku Iya Tuntubarmu Ta Wadannan Hanyoyi Kamar Haka.

Email: aminubyusuf20@gmail.com

WhatsApp: +2347010942309

Facebook: Arewa Talent

Instagram: ArewaTalent.Com.Ng

YouTube Channel: Arewa Talent Tv

Comments

  1. Allah Yakara basira, daukaka da albarka.
    Hakika nakaru matuka.
    Nagode kwarai.
    Allah Yasaka da alkhairi.

    ReplyDelete

Post a Comment