[WhatsApp]: Yadda Zaka Sakawa WhatsApp Dinka Two-Step Verification 2020.

whatsapp two step verification

Barka da zuwa shafin Arewa Talent, A wannan lokaci Insha Allahu zamu nuna maka yadda zaka sakawa whatsApp dinka two-step verification. Abinda yasa zamu nuna maka wannan abu saboda dayawan mutane ana kwace musu account dinsu na whatsApp, Amma tayaya zaka kare kanka daga masu kutsen whatsapp.

Read more: [WhatsApp]: Abubuwan da Suke Sawa WhatsApp su Dakatar da Mutum Daga Yin Amfani da Manhajarsu Ta WhatsApp.

Menene two-step verification?

Two-step verification wani tsarine da zai karawa account dinka na whatsapp security sosai. Kuma zai baka damar kayi creating na PIN da lambar wayarka ta whatsApp, Saboda idan wani yayi attempting din bude whatsApp da lambar wayarka to za’a sanar da kai da wuri.

Tayaya Ake Saka Two Step Verification?

Step 1: Abu na farko da zaka farayi shine zaka shiga cikin account dinka na whatsapp bayan ya bude maka daga sama a gefan hannunka na dama zaka wasu Dot-dot guda uku saika dannasu bayanka danna zai baka wasu rubutu guda biyar saika shiga inda aka saka Setting.

Step 2: Abu na biyu da zaka karayi shine bayanka danna Setting acikin gurin daya bude maka zakaga wani guri ansa Account saika danna shi kana dannawa zai shigar da kai wani guri a inda ya shigar da kai zakaga wani rubutu ansa Two-step verification saika danna.

Step 3: Abu na uku da zaka karayi shine bayanka danna Two-step verification zai kawo ka wani guri ansa Enable saika danna shi kana dannawa zai baka damar kasaka PIN guda shida kana sakawa zai dada baka damar ka maimaita PIN din daka saka a baya.

Step 4: Abu na hudu da zaka karayi shine bayanka gama saka PIN guda shida zai kuma baka damar idan kana da Email Address zaka iya sakawa, idan kuma baka dashi saika kyaleshi.

Idan duk kagama saka wadannan abubuwa shikenan ka sakawa account dinka na whatsApp two-step verification kuma ka dadawa account dinka security sosai, Saboda yanzu duk wanda yayi attempting din shiga whatsApp dinka za’a sanar da kai.

Read more: [Apps & Games]: Yadda Ake Hada Cartoon Animation Video 2020.

Read more: [Blogging]: Darasin Koyon Blogging Kashi Na Biyu 2020.

Read more: [Gmail Account]: Yadda Ake Bude Gmail Account 2020.

Read more: [Recruitment]: Abubuwan da Ake Bukata Idan Zaka Nemi Aikin Nigeria Police Force 2020.

Ku Kasance Da Arewa Talent A Kowane Irin Lokaci Muma Zamu Cigaba Da Kawo Muku Abubuwa Wanda Zaku Dinga Karuwa Dasu Kuma Kuna Jin Dadinsu, Nine Naku Aminu B Yusuf CEO Founder Na Arewa Talent.

Domin Neman Karin Bayani Ko Kuma Bamu Wata Shawara Akan Wani Abu Zaku Iya Tuntubarmu Ta Wadannan Hanyoyi Kamar Haka.

Email: aminubyusuf20@gmail.com

WhatsApp: +2347010942309

Facebook: Arewa Talent

Instagram: ArewaTalent.Com.Ng

YouTube Channel: Arewa Talent Tv

Comments