[Blogging]: Menene Ma’anar Google AdSense Da Kuma Abubuwan Daya Kunsa 2020

how-to-make-money-with-adsense-2020

Barka da zuwa Shafin Arewa Talent a wannan lokaci Insha Allahu zamu fadamuku yadda ake amfani da Google AdSense da kuma abubuwan daya kunsa.

Menene Google AdSense?

Google AdSense wani tsarine wanda kamfanin Google suka fito dashi wanda kaf acikin kamfanunuwan da suke bada talla a website babu kamar Google AdSense kai harma a wajen biyan kudi babu wanda ya fishi, Wanda idan harkana da Website ko kuma YouTube Channel kana yin posting acikinsu to zaka iyayin rijista da Google AdSense harma kafara samun kudi dashi.

Read more: Yadda Ake Bude YouTube Channel 2020

Menene Ma’anar Yin Amfani da Google AdSense Acikin Website?

Ma’anar yin amfani da Google AdSense acikin website shine idan kana amfani website dinka kuma kanaso kafara samun kudi da wannan website din naka to zaka iyayin rijista da Google AdSense domin kafara samun kudi.

Amma katabbatar website dinka yana da akalla posting guda 30 kuma katabbatar rubutun da yake cikin website din na kane bana wani ka dauko ba.

Katabbatar a website dinka kasaka wadannan abubuwa guda hudu wanda ake kiransu da About Us, Contact Us, Privacy Policy, Sitemap wadannan abubuwa suna iya taimakama wajen Google AdSense su amince da website dinka.

Menene Ma’anar Yin Amfani da Google AdSense a YouTube Channel?

Ma’anar yin amfani da Google AdSense a YouTube Channel shine idan har a YouTube Channel dinka kana da Subscribe dubu daya (1000) kuma kana da Watch Hours dubu hudu (4000) to zaka iyayin rijista da Google AdSense harma su fara biyan ka kudi.

Amma abinda zaka lura dashi acikin YouTube Channel shine kada kasake kadinga daukar bidiyon wani kana sakawa a Channel dinka saboda yin hakan zai iya bawa YouTube Channel dinka matsala sosai.

Rubutu Masu Alaka

Read more: [Blogging] Darasin Koyon Blogging Kashi Na Farko 2020

Read more: [Blogging] Darasin Koyon Blogging Kashi Na Biyu 2020

Read more: [Blogging] Wana Abubuwa Yakamata Kasani Yayin da Zaka Fara Sana'ar Blogging 2020 

Domin neman karin bayani ko kuma bamu wata shawara akan wani abu zaka iya ajiye mana comment a kasa ko kuma ka tuntubemu ta wadannan hanyoyi kamar haka.

Email: aminubyusuf20@gmail.com

WhatsApp: +2347010942309

Facebook: Arewa Talent

Instagram: ArewaTalent.Com.Ng

YouTube Channel: Al'ameen Tech

Comments

Post a Comment