Barka da zuwa shafin Arewa Talent a wannan lokaci Insha Allahu zamuyi muku bayani game da wani sabon salon cuta ko kuma muce ha’inci da kuma yaudara da wasu bata gari suka bullo dashi domin cutar da al’umma.
Read more: Yusuf Maitama Sule University Kano Cut-Off Mark 2020/2021
Read More: Yadda Zaka Duba Date of Birth Dinka Dakasa a BVN Dinka 2020
Mu lura sosai wajen cirar kudi a ATM Machine
Wannan salo
na damfara daya faso kai cikin al’umma yana faruwa ne a yayin da mabukacin dake
son cire kudi a jikin ATM Machine da katinsa a nan ne inda idan mutum ya sanya
wannan kati nasa cikin injin ATM idan yasami ya wani dan tangarda na Service ko
kuma ba kudi acikin ATM din to sai kaga wani mutum a gefe ya taso yazo kusa
dakai da zarar ya fuskanci kadan sami matsala da zummar yayima taimako ta inda
zai fara tambayarka “Malam ba kudi ne ko bakasa katin dai-dai bane”? to daka
bashi dama zaiyi kokarin tambayarka meye PIN din katin naka wato ATM CARD PIN? To
idan ka bashi sai yayi gaggawar musayama katin naka da wanda ba naka ba, Misali
idan katin ATM dinka na kamfanin GTbank ne shima yana makale da na GTbank din a
hannunsa daya karbi naka saiya musayama dana hannun nasa wanda yarigaya yayi
Expire ko kuma na wani ne suka karba to yan mintina kadan sai ya bace a nemeshi
a rasa inda tini zai garzaya ATM Machine na nesa dakai inda saidai kadinga jin Debit
Alert ma’ana ana ta kwashema kudi kenan kafin ka farga an yashe kudaden dake cikin
Account dinka tsaf! To Allah ya
kiyashemu ya kuma kare Al’ummar mu ta Nigeria baki daya.
A nan Arewa Talent tana baiwa al’umma shawara duk yayin da mutum yaje bakin ATM Machine da ya dinga kula sosai, Sannan idan da wani abu da bai fahimta ba to ya nemi Security na bankin domin ya warware masa matsalarsa ko kuma ya shiga banki wajen Customer Care domin ya sami cikakken bayani.
Rubutu Masu Alaka
Read more: Bashi Wanda Babu Ruwa Kwatata Acikinsa 2020
Read more: Yadda Ake Dawo da National ID Card Idan Yabata ko An Sace
Read more: Kokasan Tayaya Zaka Samu Kudi Da Tsarin InksNation
Read more: Nigeria Police Force Physical Screening Exercise 2020: Date/Time
Domin neman karin bayani ko kuma bamu wata shawara akan wani abu zaka iya ajiye mana comment a kasa ko kuma ka tuntubemu ta wadannan hanyoyi kamar haka.
Email: aminubyusuf20@gmail.com
WhatsApp: +2347010942309
Facebook: Arewa Talent
Instagram: ArewaTalent.Com.Ng
YouTube Channel: Al'ameen Tech
Comments
Post a Comment