SAMA DA 40,000 NA KANANU DA MATSAKAITAN MASANA’ANTU NE SUKA NEMI TALLAFIN PAYROLL FUND

 

Adai-dai lokacin da  aka  rufe shirin Payroll Support  na Gwamnatin Tarayya  akwai kimanin  Masana’antu, Kungiyoyi da Makarantu  432,000 ne suka nemi  wannan Tallafi amma saidai dubu saba’in ne 70,000  suka cika dukkan abinda ake da bukata a lokacin rijistar.

Ofishin dake kula da wannan shiri (Project Delivery Office) dake karkashin karamar ministan masana’antu da kauwanci (Minister of state for industry, trade and Investment). Ambassador Maryam Katagum takara da cewa Zasu biya Ma’aikatane kai tsaye amma bata hanyar masu mallakin kanfani ba.

READ MORE: ShirinGwamnatin Tarayya Na Yiwa Sana’o’i Rijista Kyauta Ya Fara

Bayan rufe wannan tsari  15 ga October 2020, mafi yawancin jihohi basu cika adadin da aka basu ba hakan yakaida anata neman da akara lokacin domin ko wacce Jiha ta iya cimma adadin da aka bata.

Akarshe Hukumar takara dacewa shi wannan tsari na Payroll Support  ya ta’allakane akan gwargwadon bayanai da wadanda  suka nema suka  bayar.

#EndSARS!

 

 

 

Comments