Shin Koka Karbi Kudinka Na Tsarin InksNation?

Shin Koka Karbi Kudinka Na Tsarin InksNation?

A yau ne kimanin wata biyar kenan ko shida da jama’ar kasar nan daga sassa  daban-daban suka gudanar da rijistar InksNation a inda wasu daga cikin mutane aka basu wasu ‘yan kudade wanda bai taka kara ya karya ba.

Hakan ya janyo hankalin wasu mutanan sukai ta cigaba da danna kudaden su da sunan suna jiran su kwashi 2.7 million ba caas ballantana aas!

To amma abin bammamaki shine yana da kyau mutane su fahimci cewa ba zata sabu ba kashuka duma ba sa’annan kuma katsuguna kadauki kabewa ba! Domin komai da akwai muhallinsa.

Also read: Kokasan Tayaya Zaka Samu Kudi Da Tsarin InksNation 

Tun a baya Arewa Talent Team sunyi dogwan nazari da buncike akan shi wannan tsari na InksNation kuma mun bada shawara sosai akan cewa duk wani tsari da bashi da alaka da babban bankin kasa Central Bank of Nigeria (CBN) ko kuma bankuna da muke dasu a wannan kasa tamu mai albarka, To baikamata mutum ya toshi kunnansa yayi tsalle ya danna kansa cikin kogin da bazai iya fita ba.

Arewa Talent Team duk da haka basu hakura ba wajen bincikowa al’umma gaskiyar lamari kamar yarda muka tattauna da wani mutum dayayi rijistar, inda yace: “Nayi wannan rijista ta InksNation kimanin wata 5 da suka wuce ina ta jira na karbi kasona amma tsiit! Kakeji kamar an shuka dusa! Na gano cewa lallai wahalar banza nayi dana zauna dafawa rakumi shayi tun da gani rike da wani kati da InksNation suka bani amma ya zamimun tamkar katin karta tun da dai bazan sanya shi bisa injin bada kudi na ATM ba to kunga bai da wani amfani.”

Karshen hirarmu kenan da wani Mutum dayace kar a baiyana sunansa, A karshe Arewa Talent na kara baiwa al’umma shawara dasu ringa kula da kuma tambayar masana akan dukkan wani al’amari daya shigema duhu domin gujewa cizan yatsa da kuma dana sani fatan alkhairi.

Comments

  1. Please I want know if students wallet is accredited by the CBN,can we enrol?

    ReplyDelete

Post a Comment