Bisa yadda “yan yahoo yahoo ke baza hajarsu ta kirkiraro forms suna sanya suna ko logo na gwamnati domin a amince dasu yasa Arewa Talent ta kara azama don fadakar da mutane kan wani sabon website dake yawo a social media fgn-grant.freefunds.xyz a cikin wannan website zaka abubuwa kamar haka:
- Gederal Government Grant
- Se form da zaka cike
Bayan ka cike wannan form zasu rubuto maka
“We congratulate you we choose you to give you a chance to be a part to benefit from the 75 billion federal Governmet Grant. Left only 8560 available slots for the federal Governmet Grant”
- To start a new business
- To pay my bills
- To support my existing business
Daga nan zaka cika izuwa karshe a inda zasu umarce ka da ka turawa mutum 12 dake kan whatsApp dinka.
Yanada kyau mutane su ringa dubawa, babu wata sheda ko lambar waya ko email dake nuna alakar wannan website (fgn-grant.freefunds.xyz) da gwamnati ko wata halartacciyar kungiya (NGO) Arewa talent na jan hankalin jama’a dasu kara kulawa da irin wadannan miyagu domin kada wajan neman gira a rasa idanu.
Comments
Post a Comment