Yadda Zaka Gane Npower Portal Na Gaskiya Dana Bogi


Npower programme shirine da gwamnatin Nigeria ta samar domin tallafawa matasan kasar wanda ya hadar da Maza da Mata, wanda tuni batch A da B suka kammala nasu shirin.

Amma abin takaici wadansu da ba’asan ko suwaye ba sun fito da wani portal na karya a inda suke amfani da logo na Npower suna sace bayanan mutane domin cutar da al’umma.

Yana da kyau mutane su ringa kula a yayin da sukaga an turo musu wani Link la’allah ta Facebook ne ko ta WhatsApp kada suyi saurin yin rijista ko turawa izuwa wani Group har sai sun tantance aya da tsakuwa.

Wannan portal da Arewa Talent ke Magana akansa lallai akwai hatsari da kuma kasada ga duk wanda ya dure bayanansa na bankinsa. https://n-power.freefunds.xyz a kula bashine wanda gwamnati ta samar ba, saboda kuna shiga cikinsa zakuga bayanai kamar haka na jikin hoton dake kasa.

Idan kuma kadanna Check zai kaika izuwa wajen da zaka sanya Account Number da kuma sunan bankinka.


Da zarar ya kammala ba’asan kuma me zai faru a gaba ba dan haka jama’a a kiyaye Allah kuma ya karemu.

Wannan shine portal din Npower na gaskiya https://nexit-fmhds.cbn.gov.ng/auth/signup wanda za’a bada tallafawa wadanda sukayi Npower programme a baya.

Domin Karin Bayani: 07010942309    


Comments