Barka da zuwa shafin Arewa Talent a wannan lokaci Insha Allahu zamu fadamuku gameda wani tsari da yake ta zagaye a wannan kasa tamu lungu da sako musamman a jihohin mu na Arewa, a inda zakaga mutane sunyi dafifi ko sunyi kawanya a shagunan masu kafe (Cafe) da zummar ayi musu wannan ta rijista ta InksNation.
InksNation - One United Global Family
A inda zaka
biya naira dubu daya da dari bakwai N1700 kudin rijista sannan kuma bayan
kammala rijista ta InksNation saika koma gefe kana daga gida a kwance ba aikin
fari bare na baki saika dinga kwasar kudi duk karshen wata ko sati-sati, sannan
za’a baka katin shaida na plastic mai dauke da hotanka da wasu lambobi akansa,
wanda akace zaka iya cire kudi dashi AMMA FA AKULA domin shi wannan kati da za’a
baka bashi da alamar da zaka iya sanya shi cikin injin bayar da kudi wato (ATM
MACHINE) kuma shi wannan tsari na InksNation ba wanda yaga takardar su ta
shaida ko ta sahalewa daga babban bankin kasa wato Central Bank of Nigeria (CBN).
Sannan
InksNation baya da wata alaka da bankunan kasar nan dan haka Arewa Talent tana
shawartar wadanda suke da sha’awar shiga wannan tsari na InksNation dasuyi duba
sannan su buncika kuma suyi nazari kafin suyi rijista da wannan tsari na
InksNation muna fata jama’a zasu tattare hankulansu waje daya domin tantance
aya da tsakuwa.
Daga
Mustapha Salisu masanin hada-hadar kudi na yau da kullum.

Good job
ReplyDeleteThanks
DeleteGood aidia
ReplyDeleteThanks
DeleteNaji dadin bayanan da na samu a Arewatelent
ReplyDeleteGaskiya kun Kyauta DA wannan bayanin Allah ya Kara basira Amin
ReplyDeleteAmeen bro
DeleteMuna,maku fatan alhairi da,nasara Allah yaqara daukakaku.
ReplyDeleteMuna godiya bro
DeleteNa ji dadin wannan shafi naku duk da cewa yau na fara shiga, na gamsu da irin bayanan ku. Allah ya yi jagora
ReplyDeleteAmeen bro
DeleteGood
ReplyDeleteThank you
DeleteArewa talent Allah ya zaka da alkhairi.
ReplyDeleteAmeen bro
ReplyDeleteAllah yayi jagoranchi.
ReplyDeleteAl'ameen.
Ameen
DeleteAllah ya dafamana kasa mudace mu km gama lpy AMEENππ½
ReplyDeleteIna yi muku fatan alkhairi a rayuwa.
ReplyDeleteMaddallah da wayarwa da mutana Kai da kake Area talent
ReplyDeleteMuna godiya Allah ya Kara basira
ReplyDelete08166119160
ReplyDeleteThanks
ReplyDeleteMuna karuwa matuka daku
ReplyDeleteMuma Muna Godiya Sosai
DeleteWanna gaskiyane Amma dae akwai lauje cikin nadi
ReplyDeleteAllah yataimaka
ReplyDeleteTsakani da Allah ninayi wannan rijistar kuma har yanxo banji alat din kumai back
ReplyDelete