Kokasan Tayaya Zaka Samu Kudi Da Tsarin Inksnation

what is inksnation

Barka da zuwa shafin Arewa Talent a wannan lokaci Insha Allahu zamu fadamuku gameda wani tsari da yake ta zagaye a wannan kasa tamu lungu da sako musamman a jihohin mu na Arewa, a inda zakaga mutane sunyi dafifi ko sunyi kawanya a shagunan masu kafe (Cafe) da zummar ayi musu wannan ta rijista ta InksNation.

InksNation - One United Global Family

A inda zaka biya naira dubu daya da dari bakwai N1700 kudin rijista sannan kuma bayan kammala rijista ta InksNation saika koma gefe kana daga gida a kwance ba aikin fari bare na baki saika dinga kwasar kudi duk karshen wata ko sati-sati, sannan za’a baka katin shaida na plastic mai dauke da hotanka da wasu lambobi akansa, wanda akace zaka iya cire kudi dashi AMMA FA AKULA domin shi wannan kati da za’a baka bashi da alamar da zaka iya sanya shi cikin injin bayar da kudi wato (ATM MACHINE) kuma shi wannan tsari na InksNation ba wanda yaga takardar su ta shaida ko ta sahalewa daga babban bankin kasa wato Central Bank of Nigeria (CBN).

Sannan InksNation baya da wata alaka da bankunan kasar nan dan haka Arewa Talent tana shawartar wadanda suke da sha’awar shiga wannan tsari na InksNation dasuyi duba sannan su buncika kuma suyi nazari kafin suyi rijista da wannan tsari na InksNation muna fata jama’a zasu tattare hankulansu waje daya domin tantance aya da tsakuwa.

Daga Mustapha Salisu masanin hada-hadar kudi na yau da kullum.

Comments

  1. Naji dadin bayanan da na samu a Arewatelent

    ReplyDelete
  2. Gaskiya kun Kyauta DA wannan bayanin Allah ya Kara basira Amin

    ReplyDelete
  3. Muna,maku fatan alhairi da,nasara Allah yaqara daukakaku.

    ReplyDelete
  4. Na ji dadin wannan shafi naku duk da cewa yau na fara shiga, na gamsu da irin bayanan ku. Allah ya yi jagora

    ReplyDelete
  5. Arewa talent Allah ya zaka da alkhairi.

    ReplyDelete
  6. Allah ya dafamana kasa mudace mu km gama lpy AMEENπŸ™πŸ½

    ReplyDelete
  7. Ina yi muku fatan alkhairi a rayuwa.

    ReplyDelete
  8. Maddallah da wayarwa da mutana Kai da kake Area talent

    ReplyDelete
  9. Muna godiya Allah ya Kara basira

    ReplyDelete
  10. Wanna gaskiyane Amma dae akwai lauje cikin nadi

    ReplyDelete
  11. Tsakani da Allah ninayi wannan rijistar kuma har yanxo banji alat din kumai back

    ReplyDelete

Post a Comment